Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Nafisa Abdullahi ta yabi Saurayin da yake rabawa ‘yan makaranta tallafi domin soyayyar da yake mata

Jaruma Nafisa Abdullahi ta yabi Saurayin da yake rabawa 'yan makaranta tallafi domin soyayyar da yake mata

Shankoko daukar rai in ji Hausawa Mun sha jin
labarai na abubuwan Al’ajabi da mutane keyi dan nuna soyayyar su ga yan film ko yan siyasa
musamman ma dai yan film din kuma mata jarumai.

Advertising

Irin su Momy Gombe Maryam Yahaya Fati muhd
Adam A Zango Nura M Inuwa Umar m shareef da Sauran su, sun sha cin karo da masu nuna musu abubuwan mamaki sabida soyayya musamman ma Maryam Yahaya da har da wanda yasha fiyafiya sabida kawai yazo bai samu ganin ta ba.

Haka zalika akwai wanda ya yanke jiki ya fadi
sa’ilin da yayi ido biyu da Adam A Zango da sauran Abubuwan mamaki da suka faru masu kama da wannan, daga yan kallo ga wayan da suke kauna cikin masu harkar nishadi.

Shiko wani matashi dan jahar Bauchi mai suna AA Asheer dake matukar kaunar jarumar shirya
finafinai Nafisat Abdullahi yazo da wani sabon
salon nuna soyayya shi ba kuka ya yi ba, bai niki gari yazo kano ko kaduna ko jos ganin ta ba bai sha fiyafiya ba haka zalika bai zana sunanta a jikin shi ko a rigar sa ba.

Advertising

Hotunan ta yake bugawa a jikin littattafai da kayan karatu jakunkunan makaranta da sauran su yana rabawa a islaniyyoyi da makarantun boko kawai sabida soyayyar sa da Nafisat.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga irin abubuwan da Saurayin yake rabawa ‘yan Makarantar sabida soyayyar da yake wa jaruma Nafisa Abdullahi.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button