Labarai
Yanzu-yanzu: Anga watan Azumin Ramadan a kasar Saudiyya
Yanzu-yanzu: Anga watan Azumin Ramadan a kasar Saudiyya
Kasar Saudiyya ta sanar da ganin watan Ramadan na Shekarar 1443 a yau Juma’a, hakan na nuni da cewa gobe Asabar za’a fara azumin watan Ramadan din a kasa mai tsarki.
Advertising
Kafar yada labarai ta Haramain Sharifain da ke Saudiyya ce ta sanar da hakan a Sahihan shafukanta na Facebook da Twitter.
Haka zalika Daily Nigerian Hausa ta tuntu bi wasu ‘yan Nijeriya da ke zaune a Saudiya, inda suka tabbatar da cewa an sanar da ganin watant a kasar.
A yau Juma’a 29 ga watan Sha’aban kuma ita ce ranar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad ya bada umarnin a fara duban watan na Ramadan a Nijeriya.
Advertising
Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.
Advertising