Advertising
Advertising
Labarai

A guji almubazzaranci kuma masu hannu da shuni su ciyar da mabukata a wannan watan na Ramadan, cewar Shugaba Buhari

A guji almubazzaranci kuma masu hannu da shuni su ciyar da mabukata a wannan watan na Ramadan, cewar Shugaba Buhari

Kamar yadda shafin Daily Nigerian Hausa suka ruwaito cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu hannu da shuni da kada suyi almubazzaranci na abinci, sannan kuma su ciyar da talakawa mabukata.

Advertising

Buhari yayi wannan kira ne a sakonsa na azumin watan Ramadan kamar yadda sauran shugabannin duniya suka mika nasu sakunan.

Buhari, a sanarwar da kakakinsa Garba
Shehu ya fitar a jiya Juma’a a Abuja, a cewar Buhari watan Ramadan wata ne da yake sanya wa idan an ji yunuwar azumi za’a tuna yadda talaka yake fama da yunwa, inda ya kara da cewa hakan zai sa shugabanni suji yadda wahalar yunwa take.

Daga nan ne sai Shugaban kasar ya shawarci
al’umma da kada su rika almubazzaranci da
abinci da kuma kashe-kashen kudi na ba gaira ba dalili, inda ya yi kira da a rika taimaka wa makwabta da talakawa.

Advertising

Ya kuma yi kira da a dage da addu’ar neman
zaman lafiya a kasa da ma duniya baki daya, inda ya yi wa al’ummar Musulmi a fadin duniya fatan kammala kwanaki 30 na Ramadan cikin koshin lafiya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button