Advertising
Advertising
Labarai

Idan ba’a dauki matakin gaggawa ba zamu dauko Sojojin haya su yaki ‘yan ta’adda, cewar Gwamna Nasir El-Rufa’i

Idan ba'a dauki matakin gaggawa ba zamu dauko Sojojin haya su yaki 'yan ta'adda, cewar Gwamna Nasir El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi barazanar kawo sojojin haya daga kasashen waje domin yakar ‘yan ta’addan dake ta’addanci a dazuzzukan jihar Kaduna, idan gwamnatin tarayya karkashin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta gaza magance ta’addancin.

Advertising

Nasir El-Rufai wanda ya zanta da ‘yan jarida jim
kadan bayan bayyana wa Shugaban kasa kashe kashen da aka yi a jihar Kaduna, da suka hada da harin bam da aka kai ranar Litinin a layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara tare da sace wasu mutanen da har yanzu ha a san adadinsu ba.

Da yake magana da Hausa, El-Rufai ya ce:
Na je na gana da Shugaban kasa kuma na
rantse da Allah idan ba’a dauki mataki ba, mu gwamnoni zamu dauki matakin kare rayukan al’ummarmu.

Idan ta kama mu dauko sojojin haya na kasashen waje suzo su yi aikin, zamu yi hakan ne don magance wadannan kalubale.

Advertising

Sai dai kuma Nasir El-Rufai wanda yace, shugaban kasar ya tabbatar masa da cewa za’a dauki matakin kawo karshen ta’addanci nan da
‘yan watanni masu zuwa.

Ya bayyana cewa, hanya mafi dacewa da za’a magance ta’addanci gaba daya ita ce sojojin Najeriya suyi luguden bama-bamai a daukacin
maboyar ‘yan ta’adda a cikin dazuka.

Da yake magana kan harin da aka kai a ranar
Litinin a layin dogo yace, sun zo a shirye kuma sun dade suna shiri kuma sun san taragon da zasu kai hari, shine na manyan mutane kuma sunkwashi na kwasa suka tafi da su.

Kuma na dade ina cewa, dazuzzukan da wadannan ‘yan fashin ke buya, lokaci ya yi da
Zamu je can mu jefa bama-bamai duka a kashe duk wanda ke cikin dajin.

Sai dai idan ba’a yi haka ba, wannan matsalar
zata dore kuma tana iya ruguza Najeriya baki
daya.

Mun sami rahoto daga Daily Nigerian Hausa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button