Sukar Shugaba Buhari akan harin jirgin kasa Abuja Kaduna tasa an dakatar da Limamin masallacin Apo, Sheikh Khalid.
Kwamitin gudanarwa na Masallacin Juma’a na Apo da ke Abuja ya dakatar da Babban Limamin masallacin, Sheikh Nuru Khalid, saboda sukar da ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harin bam na jirgin kasa na Kaduna.
Limamin, a cikin huÉ—ubarsa ta jiya Juma’a, ya soki shugaban kasa kan gazawar sa ta zuwa Kaduna don jajanta wa wadanda harin ta’addancin da aka kai ya rutsa da su.
Ya ce shugaban ya je Kaduna domin yakin neman zabe, amma ya ki zuwa jihar bayan harin bam don ya jajantawa al’umma.
“Shugaban kasa Buhari ya ce wai yana Allah wadai, in banda su yan ta’addan, kowa ma ai yayi Allah wadai da faruwar lamarin. Ya kamata shugaban kasa ya ziyarci jihar domin jajantawa wadanda abin ya shafa”. Inji Malamin.
Sai dai kuma Shugaban kwamitin kula da masallacin, Sai’du Dansadau, ya ce an dakatar da malamin ne sabo da hudubar da yayi a ranar 1 ga Afrilu za ta iya tunzura al’umma.
Ya bayyana cewa Shehun Malamin ya yi wa’azi na hana al’umma yin abun da kundin tsarin mulkin kasa ya basu, ta hanyar shawartar masu zabe da su baiwa yan siyasa sharadi kafin zaben su.
Dansadau ya kuma kara da cewa wa’azin ya sabawa tsarin addinin Musulunci.