Uncategory

Bazamu saurarawa matasan da suke cin abinci da rana a watan Ramadan ba, cewar Hukumar Hisbah

Bazamu saurarawa matasan da suke cin abinci da rana a watan Ramadan ba, cewar Hukumar Hisbah

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano taci alwashin
saka kafar wando daya da matasa Musulmai
da suke kin yin azumin watan Ramadan.

A wani sakon murya ta kafar WhatsApp da ya
tura wa manema labarai a jiya Asabar, babban Kwamandan Hukumar, Muhammad Harun Ibn-Sina yace, Hukumar ba zasu saurara wa masu karya shari’ar Muslunci da gangan ba.

A cewar sa, duk wanda aka samu musulmi yana cin abinci da rana ba tare da wata larura ba to zai gamu da fushin Shari’a.

Ya kuma kara da cewa hukumar ba zata zuwa ido taga ana aikata badala a watan Ramadan da ma bayan sa ta kyale ba, inda yace dole ne tayi aikinta na horo da kyakkyawan aiki da kuma gani da mummuna.

Ibn-Sina ya kuma taya musulmai a fadin jihar
da kasa baki daya murnar zagayowar wata mai alfarma, inda ya yi addu’ar Allah ya karbi ibadun ya kuma kawo zaman lafiya da arziki a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button