Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin jihar Kano tayi kakkausan gargadi ga masu yin kankara da gurbacaccan ruwa A Ramadan

Gwamnatin jihar Kano tayi kakkausan gargadi ga masu yin kankara da gurbacaccan ruwa A Ramadan

Hukumar Kare Hakkin mai Sayen Kaya ta jihar Kano CPC tace, ba zata saurarawa duk wanda aka samu yana hada kankara da gurbataccen ruwa ba, musamman a watan azumin Ramadan.

Advertising

Shugaban Hukumar, Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ofishin sa.

Danbazau, wanda Daraktan kula da Aiyuka na
Hukumar Dr.

Tijjani Jafaru ya wakilta yace, sun fahimci a lokacin azumin ana hada kankara da gurbataccen ruwa, wanda kuma yin hakan ya
saba wa dokokin hukumar.

Advertising

Yace, sun samar da wani kwamiti mai karfi, wanda zai gudanar da bibiyar yadda masu sayar da kayan abinci da kayan sha zasu gudanar da harkokin su lokacin Azumin Ramadana.

Bayan Amfani da gurbataccen ruwa akwai kuma wadanda suke gudanar da yin kankara a wuri da yanayi maras tsafta.

Kuma su kan su wadanda suke kula da wajen duk wadannan baza mu saurara musu ba, Inji
Danbazau.

Janar Danbazau ya kuma bukaci al’umma da
su rika sanar da Hukumar duk wani wajen da
suka ga ana hada wa da sayar da kayan cikin kazanta, da kuma inda ake tauye mudu da sayar da gurbatattun kaya musamman kayan lemo ko kayan marmari.

Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button