Advertising
Advertising
Labarai

Har yanzu babu bayanin fasinjoji 192 wanda aka sace a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, cewar RNP

Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen Kasa ta
Kasa, NRC, ta tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji kusan 170 daga cikin 362 da aka tabbatar da su a cikin jirgin AK9 dake Abuja zuwa Kaduna.

Advertising

A ranar 28 ga Maris wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari kan jirgin kasan da
bama-bamai a yammacin ranar.

Ko da yake jimillar kujerun jirgin ya 840 ne amma sahihan fasinjoji a jirgin 362 ne Jirgin ya kunshi ingantattun fasinjoji 362 ne.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta tabbatar da
mutuwar mutane takwas, inda wasu fasinjoji
26 suka jikkata yayin harin.

Advertising

Da yake bayar da sanarwa a yau Asabar, Fidet Okhiria, Manajan Daraktan NRC, yace kamfanin ya hada gwiwa da hukumomin da abin ya shafa don ganin an ceto sauran fasinjojin.

Kamfanin, a cigaba da kokarin da take yi ta
hanyar kiraye-kirayen data yi, ta samu nasarar tabbatar da lafiyar fasinjoji 170, yayin nasarar tabbatar da lafiyar fasinjoji 170 yayin da fasinjoji 21 suka bace daga ‘yan uwan da suka yi mana waya.

Kamfanin yana matukar hada kai da jami’an tsaro wadanda tuni suka fara aiki bisa ga umarnin shugaban kasa na yin duk mai yiwuwa don ceto duk wadanda suka bata, in ji shi.

Okhiria ya bayyana cewa, kamfanin ya kuma
kwashe kayan jama’a da kayan masarufi zuwa wurin da hatsarin ya afku domin tabbatar da komawa aikin jirgin kasa ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce, an dauki matakin ne domin rage radadin da fasinjojin ke fuskanta a halin yanzu wajen zuwa wuraren da suke zuwa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button