Labarai
Sunan Allah ya bayyana a fuskar Sheikh Dahiru usman Bauchi..
A jiya ne da yamma, al-umma musulmai na Afrika suka fara yada hoton Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda aka zagaye jijiyoyin sa wanda yayi kama da zanen sunan “Allah”.
Daga ganin hoton kaima zakaga zanen jijiyoyin yayi kama da sunan Allah.
Sai dai manema labarai sunyi kokarin samun cikakken bayani daga makusanta Maulana Shiekh Dahiru Usman Bauchi amma abun yaci tura.
Duk da kowa yasan Shiekh Dahiru Usman Bauchi ba karamin Mallami bane a Afrika wanda wasu ma sun tabbatar da cewa Shehin Waliyyi ne.
Har kawo zuwa yanzun babu wani makusancin sa daya ce wani abu a game da lamarin, Masu bibiyar mu muna jiran ra’ayoyin ku akan wannan abu.