Advertising
Advertising
Labarai

Ƴan sanda sun ƙi karɓar cin hancin N500,000 bayan da su ka kama motar bas ɗauke da miyagun kwayoyi a Legas

Jami’an Rundunar Ƴan sanda ta Kan-ka-ce-kwabo, wato Rapid Response Squad, RRS, sun tare wata motar bas maƙare da miyagun ƙwayoyi a unguwar Mile 2 da ke Jihar Legas.

Advertising

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Legas.

Ya ce jami’an RRS sun tare motar bas din inda su ka kama Ojukwu Omanogho mai shekaru 36 da Hope Jumbo mai shekaru 40 da Oluwole Omojuyitan mai shekaru 40.

Hundeyin ya ce binciken farko ya nuna cewa magungunan na wani Alhaji ne wanda aka fi sani da Janar a unguwar Mushin.

Advertising

“Magungunan na Janar din, an yi lodin su ne a cikin wata motar bas ta LT, mai lamba AGL 205 YD a Legas.

“Duk da haka, sai su ka taki rashin sa’a lokacin da jami’an RRS da ke sintiri su ka tsayar da bas din a kan binciken da aka saba yi na yau da kullum da misalin karfe 4 na ranar Lahadi.”

Hundeyin ya ce jami’an sun ƙi karɓar cin hancin N500,000 da ga Omojuyitan, ɗaya da ga cikin gungun masu safarar ƙwayoyin.

“’Yan sandan sun kama Omojuyitan, wanda da farko ya tsere daga wurin a kan babur, bayan ya dawo da N500,000.00 domin bai wa jami’an cin hancin su sako miyagun kwayoyi da wadanda ake zargi.

Kakakin ya ce Kwamishinan Ƴan Sandan sandan jihar, CP Abiodun Alabi, ya yaba wa kwamandan RRS, CSP Olayinka Egbeyemi da tawagar bisa wannan bajinta.

Kwamishinan ya bayar da umarnin a mika wadanda ake zargi tare da kayan laifin zuwa shelikwatar rundunar domin ci gaba da bincike.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button