Abin farin cikin da bazan taba mantawa da shi ba shine ranar da Mahaifiyata ta Mutu, cewar Momee Gombe
Abin farin cikin da bazan taba mantawa da shi ba shine ranar da Mahaifiyata ta Mutu, cewar Momee Gombe
Jarumar masana’antar kannywood Maimuna Abubakar wacce aka fi sanin ta da Momee Gombe ta bayyana cewa, babu ranar da tafi shiga farin ciki da kuma bakin ciki irin ranar da Mahaifiyar ta ta rasu.
Jaruma Momee Gombe ta bayyana hakan ne a shirar da suka yi da BBC Hausa a cikin shirin nan nasu na Daga bakin mai ita, inda ta bayyana da dama suka shafi rayuwar ta.
A cikin shirar tasu an tambayi Momee Gombe abin da yake sanya ta farin ciki, sai ta bada amsa da cewa.
Abinda ya ke sa ni farinciki shi ne ibadata. Duk lokacin da na ji ina ibada, ina samun farinciki.
Bayan haka an sake tambayar ta kan cewa, menene yake sanya bakin ciki shi tace abin da yake sanya ta bakin ciki shine idan ta tuna mutuwar Mahaifiyar ta.
Zaku iya kallin bidiyon dake kasa domin kuji cikekkiyar shirar da BBC Hausa tayi da jaruma Momee Gombe.