Advertising
Advertising
Labarai

Gwamna Ganduje ya ƙi amince wa da murabus ɗin Shugaban KAROTA Babba Dan’agundi

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ƙi amincewa da takardar ajiye aiki da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi ya aika masa.

Advertising

Muƙaddashin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, shi ne ya ƙi amincewa da murabus ɗin bayan da a ka aike masa da takardar ajiye aikin, sakamakon cewa Ganduje ba ya gari.

Rahotanni sun bayyana cewa Dan-Agundi ya shirya mika takaradar ajiye aiki a yau Litinin din nan.

Jaridar Politics Digest ta rawaito cewa a yau Baffa Babba ya rubuta takaradar yin murabus daga mukamin sa, sai dai Gwamna Ganduje wanda a halin yanzu yana Dubai ya umarci Mukaddashinsa, ya ki amincewa da takardar ajiye aikin.

Advertising

Yayin da aka tuntubi shugaban hukumar KAROTA kan wannan batun ya ce “Gaskiyane na aika takardar ajiye aiki, amma mai girma Gwamna yaki amincewa.

“Ka san shi gwamna ba wai mai gida na ba ne kaɗai, shi uba ne a gare ni, sabo da haka dole na bi duk abinda ya ce min.

“Gwamna Ganduje shi ne ya bani wannan muƙamin na riƙe KAROTA kuma ya sa na samu ɗaukaka a harkar siyasa ta.

“Sabo da haka ba zan ƙi yin abinda gwamna Ganduje ya saka ni ba,” inji Dan’agundi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button