Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan bindiga sun kashe Mutane 10 tare da raunata 19 a wajan bikin al’adun Irigwe a Plateau

'Yan bindiga sun kashe Mutane 10 tare da raunata 19 a wajan bikin al'adun Irigwe a Plateau

Wasu yan bindiga sun kashe mutane 10 tare da raunata wasu 19 a wani bikin al’adu da aka yi a unguwar Chando Zerreci dake Masarautar Irigwe, Karamar Hukumar Bassa a Jihar Plateau.

Advertising

Lawrence Zango, sakataren yada labarai na kasa na Kungiyar Matasan Irigwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Jos.

Zango yace, yan bindigan sun kaddamar da harin ne a daren ranar Asabar a lokacin bukukuwan al’ada na ‘Zerreci’ na shekara shekara, wanda shine bikin su na shiga sabuwar kakar noma.

A cewar Zango, wanda ya yi Allah wadai tare da bayyana lamarin a matsayin abin takaici da bakin ciki, wadanda suka jikkata a halin yanzu suna karbar kulawa a asibitin Enos na Miango.

Advertising

Ya kuma yi kira ga gwamnati a dukkan
matakai da hukumomin tsaro da su samar da
dauwamammen mafita kan hare-haren da dauwamammen mafita kan hare-haren da suke kai wa ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Kakakin rundunar yan sandan, ASP Ubah Ogaba, ya tabbatar da faruwar harin inda ya kara da cewa, rundunar ta kai jami’anta dauke da makamai zuwa wurin domin dawo da zaman lafiya.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da ma Plateau baki daya da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda, ya kara da cewa jami’an tsaro na bakin kokarinsu wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button