Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin tarayya ta umarci kamfanonin sadarwa da su hana kira da layukan da basu da rigista

Gwamnatin Najeriya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su hana masu amfani da layukan waya yin kira da layukan su idan har ba suyi rajista sun kuma hada su da lambar zama dan kasa ba (NIN) da ga jiya Litinin.

Advertising

Hukumar kula da Harkokin Sadarwa ta Kasa, NCC tare da Hukumar kula da yin Rijistar yan
Kasa (NIMC) ne suka bayyana haka a cikin
wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar.

Wannan matakin na nufin wadanda aka rufe
layukan su sabida rashin hada su da lambar
dan kasa ba zasu iya kiran kowa ba, sai dai
za’a iya kiransu.

Ministan Sadarwa na Kasa Isa Ali Pantami ne ya bayar da umarnin.

Advertising

Gwamnatin tarayyar Nijeriya tace, kawo yanzu ta mika lambobin waya miliyan 125 domin a hada su lambar dan kasa, kuma hukumar NIMC ta yi rajistar lambobin dan kasa miliyan 78 kawo yanzu.

Sanarwar tace “Muna ba dukkan wadanda aka dode layukansu daga yin waya dasu tafi cibiyoyin da ake yin rajista domin hada lambobin nasu da lambar dan kasa, domin kamfanonin sadarwa su iya bude musu layukan nasu.

Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button