Labarai

Kimanin Mutane 7 sun rasa Rayukan su a wata gobara data tashi a gidan Mai a Kaugama jihar Jigawa

Kimanin Mutane 7 sun rasa Rayukan su a wata gobara data tashi a gidan Mai a Kaugama jihar Jigawa

Rundunar Tsaron Fararen hula ta Kasa,NSCDC, ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wata gobara da ta tashi a wani gidan mai dake Al-Masfa dake Karamar Hukumar Kaugama a Jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na “NSCDC” a Jigawa,
Adamu Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar
lamarin a Dutse a yau Talata, ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a jiya Litinin da misalin karfe 5 na yamma.

Gobarar ta kone gini dake dauke da ofisoshi da kuma wurin kwana gidan ma’aikatan gidan man.

Abin takaici, wasu daga cikin wadanda abin ya shafa na barci yayin da wasu ke hutawa,
sakamakon haka, shida daga cikin wadanda abin ya shafa sun mutu nan take yayin da daya ya cika bayan an kai shi asibiti.

Shehu ya bayyana cewa, sai da aka yi taron dangi jami’an kwana-kwana da jami’an tsaro
wajen kashe wutar data rura sosai, wanda har yanzu ba’a gano musabbabin tashin ta ba.

Ya bayyana sunayen mamatan da Nasiru Umar mai shekaru 30, Abdulkadir Nura 25, Dahawi Garin-Babale 35, Hamza Adamu15, Sulaiman Garin-Babale 35, Idris Adamu mai shekaru 40, da Salisu Garin-Babale 40.

Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button