Kotu ta yankewa Mutumin da yayi Ridda hukuncin Shekaru 24 a gidan Yari kan kalaman batanci
Kotu ta yankewa Mutumin da yayi Ridda hukuncin Shekaru 24 a gidan Yari kan kalaman batanci
Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari ga Mubarak Bala haifaffen Kano wanda ya yi ridda, bayan da ya amsa laifuffuka 18 da suka shafi tada zaune tsaye da kuma rashin zaman lafiya da ake yi masa.
Bala, wanda shi ne shugaban Kungiyar ‘Yan Adam ta Najeriya an kama shine a gidansa dake Kaduna a ranar 28 ga Afrilu 2020, kuma aka taho da shi Kano inda aka kai karar sa kotun a kan kalaman batanci ga addinin Musulunci da kuma tunzuri.
A baya dai ya wallafa kalaman batanci ga
Musulunci Allah da kuma Annabi Muhammad S.A.W a shafin Facebook, lamarin da ya harzuka Musulmai.
An dai yi kamfen a sake shi ko kuma ayi masa shari’a inda masu fafutuka ke cewa, an raba shi da samun ganawa da matarsa da iyalan sa.
Amma da ya bayyana a gaban mai shari’a Farouk Lawan na babbar kotun Kano ta 4 dake Sakatariyar Audu Bako a yau Talata, Bala ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Da alkali ya tambaye shi ko ya san sakamakon amsa laifinsa da ya yi sai Bala din ya kafe kan cewa, ya aikata laifin kamar yadda ya fada da farko.
Lauyan Bala, James Ibor, a baya ya yi kokarin
shawo kan wanda yake karewa ya sauya rokonsa, amma ya dage cewa yana da laifi kan tuhumar da ake masa.
Sai dai lauyan ya bayyana takaici da fargaba a
matsayin dalilan da suka sa wanda yake karewa ya amsa laifinsa, inda yace wanda yake karewa ya shafe shekaru biyu a gidan yari.
Sai dai kuma shi Bala din, wanda ya bayyana
a gaban kotun ba tare da tada hankali ba, ya daga hannu ya shaida wa kotu cewa ya aikata
laifin kamar yadda ake tuhumar sa.
A cikin rokonsa na neman ayi masa sassauci Bala yace, manufar rubutun da yayi a shafukan sada zumunta ba shine ya haifar da tashin hankali ba, don haka ya yi alkawarin ba zai sake maimaita irin wannan aika-aikar ba a nan gaba.
Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.