Labarai

Ramadan: An bude sabbin Zaurikan Sallah guda 80 da zadu dauki Masallata 580,000 a Haramin Makkah

Ramadan: An bude sabbin Zaurikan Sallah guda 80 da zadu dauki Masallata 580,000 a Haramin Makkah

A karo farko, an bude sabbin zaurukan sallah tamanin 80 dake cikin kashi na uku 3 na aikin fadada masallacin Harami na Makkah ga masallata a cikin watan Ramadan na wannan shekara, kamar yadda Babban Ofishin kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya sanar.

Walid Al-Masoudi, Babban Daraktan Gudanarwa na aikin fadada masallacin Harami zango na uku 3 yace, sabbin zaurukan na nan ne a kasa da kuma hawa na daya da na biyu na masallacin.

Masu ibada na iya shigar su ta kofofin shiga da dama a bangaren arewa, yamma da gabas na masallacin, da kuma babbar kofar shiga, in ii shi.

Sabbin zaurukan da aka samar zasu rika daukar kashi 95 cikin 100 na yawan zaurukan yin sallah a cikin sashen masallacin dake dauke da su, wanda a yanzu zasu iya daukar masallata har 300,000.

Idan wadannan dakunan ciki sun cika, farfajiyar arewa zata iya daukar karin masu ibada 280,000 kuma akwai sarari ma fiye da haka a farfajiyar
yamma.

Masallacin yana karuwa a cikin watan Ramadan kuma akwai tawaga da zasu tabbatar da cewa, zasu iya zagayawa, gano sabbin wuraren sallah da shiga da fita cikin sauki da aminci.

Ya kara da cewa, ana gudanar da dukkan ayyukan ne a karkashin kulawar Mohammed
Al-Jabri karamin sakataren aiyuka da fage da
kuma kare muhalli a fadar shugaban kasa,
karkashin jagorancin shugabanta Sheikh
Abdulrahman Al-Sudais.

Daidai da manufofin shugabancin Masarautar na samar da ingantattun ayyuka ga maziyartan Masallatan Harami guda biyu.

Za a iya shiga sabbin zaurukan sallar ta babbar kofar masallacin, kofar sarki Abdullah mai lamba. 100, tare da kofofi 104, 106, 112, 173, 175, da 176 a bangaren arewa, kofofi 114,116,119,121,da123 a bangaren yamma, kofofi 162, 165 da 169 a bangaren gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button