Advertising
Advertising
Labarai

Duk wanda aka kama yana aikata Daudu za’a daure shi a gidan yari a tsawon wata 6 ko aci tarar sa N500,00, cewar Dan Majalista

Duk wanda aka kama yana aikata Daudu za'a daure shi a gidan yari a tsawon wata 6 ko aci tarar sa N500,00, cewar Dan Majalista

Wani kudiri da aka gabatar a gaban Majalisar
Wakilan Nijeriya dake son ayi wa Dokar Haramta Auren Jinsi a kwaskwarima ya nemi a haramta daudu a kasar.

Advertising

Da yake karanto sashe na 4 na dokar ranar Talata, dan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Umar Muda Lawal, ya nemi a haramta daudu a fili ko kuma a boye.

Ya nemi a saka daurin wata shida a cikin dokar ko kuma tarar naira 500,000 ga duk wanda aka kama a matsayin dan daudu.

Dan majalisar naso a kara wani karamin sashe na 4 cikin baka a cikin Dokar Haramta Auren Jinsi ta 2013 da zai ayyana cewa: Duk wanda aka kama yana aikata daudu ya yi laifin da zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na wata shida ko kuma tarar N500,000.

Advertising

A jiya Talata ne ‘yan majalisar suka yi wa kudirin karatun farko, sai sun yi karatu na biyu da na uku sannan ya zama doka.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button