Advertising
Advertising
Labarai

Idan Malamai baus fadawa Shugabanni gaskiya akan Munbari ba a ina zasu fada, daga Salisu Isma’il Kabugawa

Idan Malamai baus fadawa Shugabanni gaskiya akan Munbari ba a ina zasu fada, daga Salisu Isma'il Kabugawa

Daga Salisu Ismail Kabuga.

Advertising

Ita gaskiya, gaskiya ce indai gaskiyar ce, yayin da aka tozarta gaskiya ko kuma sai an zabi wanda za’a gayawa gaskiya ma’ana sai masu rauni (Talakawa) za’a gayawa gaskiya babu shakka an tozartadda gaskiya.

Mecece gaskiya kuma a ina za’a fadi
Gaskiya?
.

takaice Gaskiya, Nasiha ce wadda ake fadawa mutum/mutane cikin zance ko a wa’azance kamar yadda Malamai keyi idan zasu warware Zare da abawa kan wani abu yayin da suke kan munbarin khudba da ma a kowanne zarafi da suka samu na fede gaskiya.

Advertising

Irin wannnan muhimmin aiki na fadar gaskiya ana iya yinsa a ko ina matukar akwai zarafin yin hakan, kuma gaskiya ta kowa ce.

Ma’ana ana iya gayawa kowa gaskiya tunda dai kamar yadda nace a takaice gaskiya Nasiha ce, ana iya yiwa Shugabanni/Masu mulki masu kudi da Malam Talaka me ye aibu idan an fadi gaskiya?.

Matukar gaskiya gaskiyar ce babu wani aibu ga dukkannin bangarori biyu wato ga wanda ya fadi gaskiya da kuma wanda aka fadawa gaskiyar, amma kuma ita gaskiya daci gare ta, domin ina iya tunawa yadda a wake Marigari Sa’adu Zungur ke fadi.

Muddun mutum ko mai wa’azi akan gaskiya yake magana to kuwa komai fadin gaskiyar ya jawo ta biya, cewar Sa’adu Zungur cikin wakensa.

Yadda malamai a dukkannin sassa suka dada zage damara wajen tunasar da Shugabanni halin da kasa ke ciki na rashin tsaro da kuncin rayuwa da ake ciki a yanzu abin a yaba ne, domin duk Dan Adam kasasshe ne a koda yaushe yana bukatar a tunasar dashi game da yin abinda ya kamata, kuma ina kyautatawa Malaman nan zaton cewa sunayi ne domin neman gyara.

Ace a wayi gari ana yiwa malamai barazarar
rabasu da wurare ko munbarorin wa’azinsu domin kawai suna isar da nasiha ga shugabanni kai tsaye daga inda suke da ikon aikewa da sako/wa’azi, yin hakan tamkar komawa zamanin jahiliyya ne.

Masu cewa, Malamai ba zasu yiwa Shugabanni Nasiha ko jan hankalin su akan munbarin karatu/Khudba ba, To a ina kuke so suyi?.

Shin kuna zaton duk wanda nasiha batayi masa dadi gada munbari ba zayi yi masa dadin ji idan gaka ga shi a fadarsa?.

Shin ko kuma kuna ganin cewa, su wadanda
ke kewaye da shugabanni da kuma ‘yan sakai
wato ‘yan jagaliyar dake kewaye da shugabannin zasu bar Malami ya samu ganin shi (shugaban) cikin karamci, domin ni dai a iya sani na a halin da ake ciki ganin shugabanni musamman na Siyasa ba sauki bare shi ba’a irin wannan yanayi da ‘yan bani na iya ke kewaye da fadar masu mulki domin kwadayin wani abu.

Haka kuma ina kuka kai tunanin da mafi yawan mutane suke yi cewa, akasarin wadanda shugabanni ke rufe kofa dasu sunje karbar nasu kason ne musamman idan aka ga Malami ne?.

A tambayi duk wani Shugaba cewa, ya yake ji idan akace gashi can Malam wane akan munbarin karatu/khudbar sa ya na fahimtar da jama’a game da wani abin alkhairi da shugaban yayi ko kuma ma ace gashi can yanayi masa addu’a tare da Dalibansa?.

Idan har yin hakan ba ketare hakkin iyakar malunta bane to ta yaya yin wa’azi gare shi akan ya gyara wani abu da yake damun Jama’a akan munbarin da ada aka yabeshi zai zama kuskure? Kuma idan har yabon da Malamai kewa shugabanni akan munbari yayin da sukayi abin yabo bai zama siyasa ba ta yaya gaya musu cewa su gyara ya zama siyasa?.

Dogaro da wannan nazari nake ganin a ka’idance dama kamata yayi ace Malamai su dinga fadin gaskiya ko wacce iri yayin da suke kan munbarin karatu/khudba domin gaskiya ta kowa ce, ala basshi idan hali ya basu dama wataran sun rabauta da ganin shugaban da suka aikawa da sakon a baya ta kan munabari to sai ku ji tsoron Allah su karasa aikin su na fadin gaskiya gaba da gaba kamar yadda ake wiya dalibai.

A gayawa Duk wani Shugaba dake ci ko ‘yan
kanzagin sa, Shin basu san cewa su MALAMAI sune magada Annabawa ba?.

Shin dama akwai abinda addini baiyi magana
Akansa ba? ko kuma ya ware cewa ba za’ayi
magana akansa ba?.

Babban aikin Malamai shine shiryadda Al’umma wajen yin dik wani abu dai-dai (politics inclusive), yadda Allah yake so da kuma yadda rayuwar Al’umma zata inganta a duniya, kuma idan akace Al’umma ba ana nufin Talaka ba kawai harda Shugabanni a kowanne mataki.

Idan har Malamai ba zasu gayawa Gwamnati
da Shugabanni indan suka gaza ba ko kuma
abinda ya zama matsalar Jama’a, to waye ya
fisu wanda zai gayawa shugabannin indai har
abinda ake tunasar dasu gaskiya ne?.

Muyi hattara Jama’a.

Kudurce jin haushin Malamai a zuci kawai kan iya hana mutum cikawa da imani domin alamune na munafunci, ballantana yinkurin
hana Malamai isar da sakon ayi dai-dai wanda aiki ne da Allah ya daura musu sabida sune masu shiryarwa tun da dai a yanzu babu Annabawa.

Gujewa Malamai ko korarsu daga Munbarin
wa’azantarwa ko shakka babu aikine irin na
Ashararai wadan da suka sanya duniya a gaba, kuma irin wadan nan mutane da ‘yan kanzaginsu da ace a lokacin Annabawa suka zo wallahi irin sune zaka ga suna futo na futo da Annabawan ko ma su kore su daga gari.

Yana daga cikin alamun rashin rabo da tabewa kaga mutum ya futo karara yana fada da gaskiya ko kuma yana kare karya da kuma jin haushin duk abinda Malamai ke fada na gaskiya.

Ko wanne musulmi wakilin Allah he a bayan kasa kuma rayuwa bata wanzuwa sai kowannen mu ya amsa tare da isar da wakilcin dake kansa ta hanyar fadin gaskiya da aiki da ita, domin Allah ne da kansa ya umarci masu Imani dasu kawarda mummunan abu da hannayen su ko da
bakunan su (wa’azi) ko kuma su kyamaci abin a zuciyoyinsu wanda shine mafi raunin Imani.

Babu shakka halin da Al’ummar Nigeria ke ciki a yanzu na kuncin rayuwa da rashin tsaro wanda ya haifar mana da zullumi da furgici a birane da kauyuka, a yanzu ne ya kamata kowannen mu ya tashi wajen yin abinda zai iya ma’ana Shugabanni nayi Malamai nayi talakawa ma nayi.

Hakika abin takaici ne matuka ace a irin wannan lokaci da kusan kowanne Dan Najeriya masu karfi da raunana wadanda ke cikin rigar mulki da wadan da ake shugabanta ke cikin rashin tabbaci sabida ba wanda ya tsira, amma ace wai a samu wasu daga cikin jama’a suna fushi da yadda Malamai ke gayawa gwamnati gaskiya a
munbarin su harma ta kai ga dakatar da wasu ko korarsu da sauya su da wanda zaiyi akasin abinda wanda aka kora yayi.

Shin waima tsakanin fushin Allah dana shugaba idan har ba akan dai-dai yake ba, wanne ne abin tsoro? Kowanne mai imani ya amsawa kansa.

Wannan ba’a matsayin irin gudummawar da
zan iya bayarwa a matsayina na Dan kasa da
kundun mulkin Nigeria ya sahalewa tofa albarkacin bakinsa, kuma banyi wannan rubutu da nufin gusgunawa kowa da kowanne bangare ba sai domin fatan ganin Kasa ta (Nigeria) ta samu zaman lafiya da bunkasar arziki ga kowanne Dan-kasa.

Allah ya fudda Kasa ta daga halin da take ciki a yanzu na rashin tsaro da furgici a dukkanin
garuruwan Arewacin Nigeria dama sauran sassa na kasar nan dama duniya baki daya. Barka da Azumi

Za a iya samun Kwamared Salisu Ismail Kabuga a kan wadan nan adiresoshi: mallamkabuga@gmail.com, 08052529040

Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button