Advertising
Advertising
Labarai

Iyalan fasinjojin da aka sace a harin jirgin kasan Kaduna sun roki Shugaba Buhari yasa baki

Iyalan fasinjojin da aka sace a harin jirgin kasan Kaduna sun roki Shugaba Buhari yasa baki

Iyalan fasinjojin da a ka sace da kuma bace wa bayan harin jirgin kasan AK9 dake kan hanyar zuwa Kaduna, sun yi kira da a sako ‘yan uwansu ba tare da wani sharadi ba.

Advertising

Idan dai za’a iya tunawa a ranar Litinin 28 ga watan Maris ‘yan ta’adda sun kai harin bam a kan jirgin kasa da ga Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe fasinjoji kusan takwas tare da yin awon gaba da wasu da dama.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya, NRC, yayin da take tabbatar da
aruwar lamarin tace, kimanin fasinjoji 392 ne ke cikin jirgin.

A cewar NRC, yayin da wajen fasinjoji 182 suka
kubuta har sun koma gidajen su fasinjoji 162 ne ke hannun ‘yan bindigar ko kuma sun bata a jeji ba’a gan su ba.

Advertising

A wata sanarwa da suka fitar a jiya Talata, shakikan fasinjojin karkashin wani gangami mai taken “Save AK9 Passengers” sun yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya shiga maganar.

‘Yan uwan wadanda abin ya shafa sun kuma
roki gwamnati data gaggauta kawo musu dauki domin fitar da wadanda abin ya shafa lafiya.

Sun kuma yi kira ga shugaban kasar da ya rika nuna damuwa da jin kai ga ‘yan kasa, musamman ma ganin cewa shi uba ne kuma kaka ne na ‘yan kasa.

Sanarwar ta ce, bayan bayanan jama’a da suka hada da bayanan jirgin ya nuna mata da yara da dama a cikin fasinjojin da aka sace.

Koken mu ya ta’allaka ne a kan cewa, da yawa daga cikin fasinjojin na fama da cututtuka daban daban da kuma magungunan ceton rai da ake bukatar sha a kullum cikin allurai.

Cututtukan sun hada da ciwon sukari, hauhawar jini da kuma ulcer, in ji Umar Abdullahi, wanda kuma ‘yar uwarsa na cikin wadanda aka sace.

Mummunan lamarin ya bar iyalai da dama cikin kunci da damuwa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button