Labarai

Tsohon shugaban kasa Jonathan Goodluck ya tsallake rijiya da baya yayin da mukarraban sa suka rasu a hadarin Mota

Tsohon shugaban kasa Jonathan Goodluck ya tsallake rijiya da baya yayin da mukarraban sa suka rasu a hadarin Mota

Jonathan Goodluck ya tsallake rijiya da baya, yayin da mukarrabansa biyu suka rasu a hadarin mota.

A jiya Laraba ne dai tsohon Shugaban Kasar
Nijeriya, Goodluck Jonathan ya yi hadari, wanda ya kai ga rasa mukarrabansa na tsaro su biyu.

Har yanzu babu cikakken bayani kan lamarin, amma kamar yadda Aminiya ta ruwaito hadarin ya afku ne a lokacin da tsohon Shugaban ke kan hanyarsa ta zuwa gidansa dake Abuja daga filin jirgin sama.

Mai taimakawa Jonathan kan harkokin yada
labarai ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace, nan ba da jimawa ba za’a fitar da sanarwa.

Da yake tsokaci kan lamarin, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar yace, wannan labari ya girgiza mu muna godiya ga Allah da ya tseratar da rayuwar Shugaban kasa @GEJonathan. Amma abin takaici ne yadda ya rasa mataimakansa biyu a hadarin mota.

Ina ta’aziyya ga iyalan marigayin da kuma Shugaba Jonathan. Allah ya jikan wadanda suka rasu ya huta lafiya, inji Atiku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button