Advertising
Advertising
Uncategory

Yadda Wani malami ya dirkawa yarinya yar shekara 12 ciki.

Wata yarinya ƴar shekara 12 a duniya wacce wani malamin makaranta yayi wa fyaɗe a unguwan Fantaro cikin ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna, a wajajen watan Yunin 2021, ta haifi ɗa namiji. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Advertising

Halima (ba sunanta na gaskiya ba) tana sayar da chin-chin, a ƙauyen su, lokacin da malamin mai suna Salihu ya yaudare ta cewa zai sayi chin-chin na N200. Salihu ya rufe mata baki sannan yayi mata fyaɗe a cikin ɗakin.

Daily Trust ta samo cewa yarinyar ta ɗauki juna biyu watanni uku bayan aukuwar fyaɗen, inda aka miƙa ta a hannun ministirin jinƙai da walwala ta hannun gidauniyar Ummulkhairi Foundation.

Hajiya Hafsat Baba ta ce:

Advertising

Ƙaramar yarinyar ta haifi ɗa namiji sati uku da su ka wuce, sannan ina farin ciki cewa likitoci a asibitin Barau Dikko sun bata kulawa ta haihu da kanta ba tare da an yi mata aiki ba.

Duk da dai jaririn yana hannun mu, mun miƙa ta zuwa wajen mahaifiyar ta ranar Laraba. Sai dai ba za mu yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin mun ƙwato mata haƙƙin ta a wurin wannan mutumin da ya jefa ta cikin wannan halin.

Ta yi nuni da cewa malamin yana garƙame a wurin hukuma tun lokacin da lamarin ya auku.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button