Advertising
Advertising
Labarai

Da’a rabawa Mutane goma Naira Miliyan 50 da’a bada a gina Masallaci da ita wanne yafi, cewar Naziru Sarkin Waka

Ficaccan mawakin masana’antar kannywood Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya wallafa wata neman shawara a shafin sa na instagram akan yadda za’a yi da Naira Miliyan 50.

Advertising

Sarkin Waka ya nema shawarar ne cikin wani dan gajeren rubutu da ya wallafa kamar haka.

Naira Milyan 50 Ce, Wai Da A Rabawa Mutane Goma Da A Bada A Gina Masallaci Da Ita Wanne Ya Fi?.

Inda aka sami Mutane da dama da suka tofa albarkacin bakin su kan neman shawara ta sa, kamar haka.

Advertising

@arewa_ premium_pics: Sarki akwai ma bukata wlh don Allah a taimaki al-ummar Annabi da Su.

@real_musanwaka : Duk Yadda Kai Daidai Ne Shakundum Babban Limaminmu. Tafiya Dai Baharin Ilminmu. Dadyn Mu Kai Kadai Aka Cewa Sarkin Waka. Shugaba Me Allah.

king_larama : A gina masallaci saboda idan aka rabawa mutum goma za suyi wani uzirin su dashi ne amma idan aka gina masallacin 50m shi Wanda ya bada kudin gina masallacin sai ya samu lada fiye da miliyan 50 kuma koh bayan ransa lada zai rinda binsa.

@hasana_muhd: A rawabawa mutum goma a gina ma sallaci yafi a gina masallaci.

@ummytah_noor : Arabawa mutum goma wata kila sanadin hakan yazama silar farincikinsu dakuma iyalansu amma kuma awani gefen gwara abawa Allah wllhy agina masallacin zaifi.

@madam_korede : Arabawa mutane mana.

@Ibrahim_birnewa : Masallatai sun yi yawa a gari.

@arewa_ premium_pics: Sarki akwai ma bukata wlh don Allah a taimaki al-ummar Annabi da Su.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button