Advertising
Advertising
Labarai

Jami’an ‘yan sanda sun kubutar da Mutane 12 da akai garkuwa da su a jihar Kogi

Jami'an 'yan sanda sun kubutar da Mutane 12 da akai garkuwa da su a jihar Kogi

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kogi ta ceto fasinjoji 12 da ga hannun wasu da ake zargin
masu garkuwa da mutane ne a jihar.

Advertising

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edward Egbuka ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a
wata sanarwa da kakakin rundunar jihar, SP William Ovye-Aya ya fitar.

Egbuka yace, mutanen 12 da abin ya rutsa dasu sun fito ne daga wata motar fasinja mai cin mutane 16 dake kan hanyar Benue, inda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka tsare motar kan hanyar Anyigba zuwa Ankpa.

CP ya ce: Rundunar ‘yan sandan ta samu wani rahoto dake nuna cewa wata motar bas Toyota mai lamba 192 XA, da wani Benard.

Advertising

Ejeh ke tuka fasinjoji 16 daga Abuja zuwa Jihar Binuwai ta hanyar ANKPA, taci karo da masu garkuwa da mutane a kauyen Ojuwo-Ajebgo na Karamar Hukumar Ofu, kan titin Anyigba.

“Ba tare da bata lokaci ba, jami’an hukumar
Quick Response Unit dake Itobe, nan take suka fara kai farmaki, suka bi sahun barayin cikin daji suka ceto fasinjoji 12 ciki har da direban yayin da ba’a ga sauran fasinjoji 4 ba.

An yi sa’a kuma, na kai ziyarar gani da ido zuwa yankin mazabar sanata ta Kogi ta Gabas, don haka lokacin da na samu labarin yayin da nake kan hanyar zuwa Ejule, nan da nan na wuce wurin, inda na gana da fasinjojin da aka ceto, in ji CP.

Egbuka, ya yi tir da rahoton karya da aka yi a
kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa, sama da Fasinjoji 15 ne suka bace sakamakon lamarin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button