Advertising
Advertising
Labarai

Direban Tasi zai shafe watanni 30 a gidan yari tare da biyan diyyar 50,000 sakamakon kade ‘yar sanda a Mota

Direban Tasi zai shafe watanni 30 a gidan yari tare da biyan diyyar 50,000 sakamakon kade 'yar sanda a Mota

Wata Kotun Majistare a ranar Juma’a ta yanke
wa wani Adelaja Ogundairo direban tasi hukuncin daurin watanni 30 a gidan yari da kuma yi wa al’umma hidima na tsawon
watanni uku bisa samunsa da laifin tukin ganganci tare da buge wata yar sanda.

Advertising

Mai laifin, a lokacin da ake shari’ar yaki amsa laifuffuka ukun da ake tuhumarsa da suka hada da tukin ganganci, kin bin dokokin hanya da kuma jikkata wata ‘yar sanda dake bakin aiki yayin da yake tuki ba tare da lasisi ba.

Alkaliyar kotun, I. O. Abudu, ta samu Ogundairo da laifi kuma ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni 12 da kuma yin hidima ta tsawon watanni uku a harabar kotun, sabida laifin tukin mota mai hatsari.

Abudu ta kuma yanke hukuncin daurin wata 12 a gidan kaso na biyu bisa tuhume-tuhume na biyu da ya hada da yi wa ‘yar sanda rauni da kuma rashin kai rahoton hadarin.

Advertising

A tuhuma ta uku, Alkaliyar kotun ta yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa samun sa da laifin tuki a kan babbar hanyar jama’a ba tare da lasisin tuki ba.

Abudu ta ba da umarnin cewa, hukuncin zaman gidan yari na watanni 30 da yiwa al’umma hidima na wata uku a lokaci guda ba tare da wani zabi na tara ba.

Ta kuma umurci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya diyyar N50,000 ga ‘yar sandan da ya kade har ta samu rauni, inda tace kudaden na magani ne data yi a lokacin jinya.

Tun da fari dai, mai gabatar da kara, Sifeto
Lawrence Olu-Balogun, ya shaida wa kotun cewa, wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a
ranar 21 ga watan Nuwamba, 2021 da misalin karfe 11:00 na safe a hanyar Lafenwa a Abeokuta.

Olu-Balogun yace, wanda aka yanke wa hukuncin ya saba wa ka’idojin zirga-zirga, ta hanyar tsayawa a tsakiyar titi da daukar fasinjoji.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button