Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Wani yaro dan shekara 14 ya rasa rayuwar sa bayan ya fada ruwa a jihar Kano
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Wani yaro dan shekara 14 ya rasa rayuwar sa bayan ya fada ruwa a jihar Kano
A wani labari da muka samu a yanzu daga shafin Daily Nigerian Hausa sun ruwaito cewa, wani yaro dan shekara 14 ya mutu a ruwa a Kano Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta
tabbatar da rasuwar wani yaro dan shekara 14, mai suna Musa Sani a wani ruwa mai suna Rafin
Mukugara dake kauyen Kumbagawa a Karamar Hukumar Karaye.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Saminu
Abdullahi ya fitar a yau a Kano yace, lamarin ya faru a jiya Juma’a da safe.
Yace, hukumar ta karbi rahoto na gaggawa a
ofishinta dake Karaye daga wani Abdulbaki
Abubakar da misalin karfe 8 na safe, inda yace nan take hukumar ta tura jami’an ta suka je wajen da misalin karfe 8:05.
Inda ya kara da cewa, an fito da yaron da ga cikin ruwan cikin halin rai-kokwai-mutu-kokwai, inda daga bisani aka tabbatar da cewa ya rasu.
Abdullahi ya kara da cewa, tuni aka mika gawar mamacin ga Dagacin Karaye, Suraja Magaji.