Mutane sun fara martani kan Ali Nuhu bisa canja Ummi Alaqa da Maryam Yahaya da yayi a shirin Alaqa din
Mutane sun fara martani kan Ali Nuhu bisa canja Ummi Alaqa da Maryam Yahaya da yayi a shirin Alaqa din
Kamar yadda kuka sani jaruma Maryam Yahaya a kwanakin baya ta dau lokaci tana fama da rashin lafiyar da taki ci taki cinyaiwa inda mutane suka ga bata fitowa a shirin masana’antar kannywood.
Inda daga baya kuma labarin rashin lafiyar tata ya riske kunne jama’a har aka fara kishi kishin samu aka yi da ita maganganu dai marasa kai da jindi, sai de daga baya kuma jarumar ta bayyana cewar typhoid da malaria ne suke damunta.
Jarumar maryam yahaya kwananan kuma cikin yarda Allah ta samu sauki har ta dawo masana’antar kannywood da cigaba da aikinta inda kwatsam aka ganta a cikin shirin alaqa an canza jaruma Habiba da Maryam yahaya din.
Tun da fari dai an bayyana kamancecceniya tsakanin Habiba wacce akafi sani da Ummi alaqa da Maryam din, kuma kamar yadda aka sani Maryam Yahaya ‘yar gaban goshin kamfani FKD Production ce kafin ta samu larurar rashin lafiya.
Kuma an fara daukar shirin alaqa ne tun lokacin tana tsaka da rashin lafiya inda mutane ke ganin daman rashin lafiyar tata ce yasa aka sa Habiba a shirin kuma da mai wuri yazo sai mai taburma ya nade kayansa.
Sai de koda da shafin dake kawo labarin shirin ya wallafa ‘ga wanda ya kalli shirin ALAQA kashi na 2 zaku ga sabuwar fuska a shirin wato Maryam Yahaya, sanan zakuji ana kiranta da Ummi ko kun lura da mai Asalin sunan!! saide Mutane sun nuna takaichin su.
El Deeny Muhammad:
Wannan zabuwa miye abun kallo a wajenta.
Ishaq Rabiu Nguru:
Gaskiya mudai bamuji dadin canja mana ita da sukayi ba.
Saide kuma daga baya shafin ya wallafa wata magana inda sukace’shirin ALAQA bashi ne shiri na farko da aka sami sauyin jaruma ko kuma jarumi ba duba da yadda aka tsara shirin tun a farko kuma abinda ake so ansamu.
Domin kwalliya ta biya kudin sabulu babu wanda zai kasa hajarsa ta sami karbuwa sannan kuma banzantar da ita hakika HABIBA Y ALIYU tana daya daga cikin wadanda suka samu tarin masoya a shirin ALAQA wanda wasu kun suke kaunar shirin domin ta yayaya za’a sauya ta ba tare da wani dalili ba ya kamata kuyi mana adalchi baza muso abinda zai bata ranku ba.