Advertising
Advertising
Labarai

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya sanar da zai tsaya takarar shugaban Kasa a 2023

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo
ya kaddamar da takarar shugabancin kasar nan a 2023.

Advertising

Osinbajo ya sanar da zai tsaya takarar ne a
wani gajeren sako da aka yada a Channels TV, bayan an shafe watanni ana rade-radi.

Ina mai sanar da ku cewa, zan tsaya takarar
Shugaban kasa a karkashin jam’iyar APC,
Idan an zabe ni, zan bada damar harkokin kasuwanci su bunkasa.

Zan bar ma’aikatun gwamnati su rika gudanar da harkoki sannan zan bunkasa shirin tallafa wa yan kasa domin kammala aikin nan na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 da ga kangin talauci.

Advertising

Sabida haka ina neman hadin kan duk wani dan kasa domin mu hadu mu ciyar da kasar nan gaba, in ji shi.

Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button