Advertising
Advertising
Labarai

Kotu ta aike da wani Mutum gidan yari bayan an kama shi da laifin yin garkuwa da Dan makwabcin sa

Kotu ta aike da wani Mutum gidan yari bayan an kama shi da laifin yin garkuwa da Dan makwabcin sa

A ranar Litinin ne wata Babbar Kotun Majistare
dake Kaduna ta bada umarnin sake tsare wani dan kasuwa mai suna Abdullahi Nurudeen mai shekaru 36 a gidan yari, bisa zargin yin garkuwa da dan makwabcinsa.

Advertising

Wanda ake zargin mazaunin titin Ali Akilu a Kaduna ana tuhumarsa da laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma garkuwa da mutane.

Mai gabatar da kara, Chidi Leo, ya shaida wa
kotun cewa, Farouq Sani na Sabon Gaya dake
Kaduna ya kai korafin ne a caji-ofis na Gabasawa a ranar 9 ga watan Fabrairu.

A cewar mai gabatar da kara, a wannan rana da misalin karfe 4 na yamma wanda ya shigar da karar ya dawo daga aiki ya gano cewa, yaronsa mai shekaru 10 da haihuwa ya bace.

Advertising

Yace, da mai karar ya tambayi wasu makwabta ko sun ga dansa, sai aka ce masa an ga wanda ake kara da wasu mutane biyu da suka tsere tare da yaron.

Daga baya wanda ya shigar da karar ya kai kara wajen ‘yan sanda kuma tuni aka kama wanda ake kara dangane da lamarin.

Leo, wani sifeton ‘yan sanda ya kara da cewa,
a yayin da ake yi masa tambayoyi wanda ake tuhumar ya amsa cewa, ya hada baki da Aminu Hassan da Barau Ahmed da a yanzu sun gudu don sace yaron.

Mai gabatar da kara yace, laifukan sun ci karo da sashe na 59 da 247 na dokar jihar Kaduna ta shekarar 2017.

Sai dai mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa, an gabatar da lamarin a gabanta ne kawai domin ta sani, sabida kotun bata da hurumin sauraren karar.

Don haka Leo ya bukaci kotun data tasa keyar wanda ake kara domin bada damar gurfanar da su a gaban kotun data dace.

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel ya bayar da
umarnin a cigaba da tsare wanda ake kara
sannan ya dage cigaba da sauraren karar har
zuwa ranar 30 ga watan Mayu, domin baiwa ‘yan sanda damar mika takardar karar zuwa ga daraktan shigar da kara na jihar domin samun shawara.

Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button