Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wani matshi dayay shigar mata ya shiga hannu a kasar Saudiya.

Wani dan kasar Masar mai suna Ahmad mai kimanin 22 ya kamu da soyayyar wata yarinya da ya nemi aurenta sau ba adadi amma bai samu karbuwa a wurin mahaifinta ba. Ahmad Ya kasance yana aiki a kasar Saudiyya.

Advertising

Tsautsayi ya sashi yanke shawarar kaiwa budurwarsa ziyara wacce ke zaune a wani kauye mai suna Sowada Abu Shalabi Al Sharqeya. Watarana ya taki sa’a budurwar ta shi ita kadaice a gida iyayenta basa nan sun fita sai Ahmad ya samu damar zuwa gareta. Wannan shawarar ziyara da Ahmad ya yanke ya aminta da ita.

Nan take ya nemi aron Abaya a wani wuri domin ya sami damar isa ga budurwarsa. Sanya abayar sa ke da wuya sai ya tunkari gidan budurwar ta sa. Amma saboda batan basira sai ya manta ya chanza takalmin kafar sa.

Allah ya halicci maza da mata da kira maban banta.Nan take mutanen kauye suka gane cewar Ahmad namiji ne hakan ya faru ne daga yanayin salon tafiyarsa da kuma takalman kafansa. Yana gab da isa gidan budurwar ta sa mutane kewayen suka dakatar da shi tare da cire Abayar jikin sa,nan take jama’ar kauyen suka farmasa da duka inda suka yi masa dukan tsiya saboda suna son tunatar da shi manufar sa akan aikata hakan.

Advertising

Yanzu dai an kama Ahmad kuma har yanzu ba a gama bincike akan faruwar wannan lamari saboda ko al’umma bata yadda da irin wannan lamari ba balle kuma hukumomi.
To matasa gareku,kunga dai yadda soyayya ta ja wa wani matashi shan na jaki.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button