Labaran Kannywood

Aure yayi albarka : Tsohuwar Jaruma Fati Ladan Tasamu Karuwa.

A safiyar Litinin, 11 ga watan Afirilun 2022 da misalin karfe 8:17 na safe, Allah ya azurta tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Fati Ladan da jariri namiji a wani asibitin kudi da ke Unguwar Rimi a Kaduna.

Idan ba a manta ba, Fati Ladan ta kai tsawon shekaru 4 da aure kafin ta samu haihuwa, wanda babu dadewa dahaihuwarsa Ubangiji ya dauki abinsa.

Sai kuma a ranar Talata, 21 ga watan Mayun 2019 Ubangiji ya kara azurta ta da haihuwar jaririya wacce aka rada wa Aisha, amma ana kiranta da Humaira. Yanzu haka saura kusan wata daya Aisha ta cika shekaru 3 da haihuwa.

Wani abin ban sha’awa da kuma mamaki shi ne an haifi Humaira a watan Ramadan ga shi wannan kanin nata ma Allah ya kawo shi da watan Ramadan.

Fati Ladan mata ce ga fitaccen dan gwagwarmayar nan kuma Shugaban Kungiyar Tuntubar Matasan Arewa, Alhaji Shettima Yerima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button