Yadda Mutane 26 suka rasu sakamakon kifewar kwale-kwale a Sokoto
Mutane 26 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da ake ci gaba da neman wasu, bayan kifewar kwale-kwale a kogin Shagari da ke Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sokoto.
Shugaban karamar hukumar Shagari, Aliyu Dantani, wanda ya shaida haɗarin ga Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN, a yau Laraba a Sokoto, ya ce lamarin ya faru ne a yammacin jiya Talata.
Dantani ya ce daga cikin gawarwakin 26 da aka kwato, 21 mata ne yayin da biyar kuma kananan yara, ya kara da cewa ana ci gaba da aikin ceto sauran fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen.
Shugaban karamar hukumar, ya ce ba a iya tantance hakikanin adadin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen ba.
A cewarsa, a halin yanzu dai masana kogi na cikin kogin don ganin yadda za a samo wasu gawarwaki ko kuma ceto wadanda suka tsira.