Advertising
Advertising
Labarai

Mutum zai iya Mutuwa ya dawo ya sake rayuwa a Dunuya cewar Ibrahim Zakzaky, (Reincarnation)

Mutum zai iya Mutuwa ya dawo ya sake rayuwa a Dunuya cewar Ibrahim Zakzaky, (Raincarnation)

Wani tsakuren video na shehin mabiya shi’a Ibrahim Yakub Alzazkzaky ya dauki hankula da yake bayyana ya yadda da mutum zai iya mutuwa ya dawo ya sake rayuwa har ya hayyafa.

Advertising

Inda ake ta tu’ajjibin wannan kalami nasa yayin da wasu kuma da suke da babbancin darika da, malamin ke karyata malamin kai tsaye da kalamai marasa da di bayan jin wannan fatawa.

Batun rija’a da malam yake magana wato reincarnation ko rebirth wani al’amari ne da duniya ta dade tana muhawara akai a tsakanin addinai da masu ilimin kimiya ne, inda wasu addinan suka tabbatar da cewa mutum zai iya rayuwa ya mutu bayan wasu shekarun kuma a sake haifar sa a wani garin ko wata nahiyar ya sake rayuwa har ya hayayyafa.

Addinan da suka fi shahara da suka kuma yi imani da wannan lamari na reincarnation sun hada da addinin Hindu, Jain da Sikhi wanda duk addinai ne na kasar india, sai kuma addinin Budda na kasar chaina da sauran kananan addinai.

Advertising

Amma manyan addinai da suka fi shahara a duniya wato Musulunci da kiristanci duk basu yadda da wannan lamari ba wanda wannna ne ma yasa batun na malamin yaja hankali matuka.

A mahangar kimiyya ma dai manazarta da masu binchike sun shafe shekaru darururwa suna son samun wata kwakwkwarar hujja da zata tabbatar da wannan batu amma kuma kawo iyanzu basu da tartibij zance gude daya da suka bayyana da zai bata dabbacin wani zai iya mutuwa ya dawo a cikin wani jikin.

Sai dai lokuta da dama cikin binciken son samun ainahin gaskiyar wannan batu akan samu yara dakan bada labari ko wasu batutuwa da suka faru abaya da kan iya sa adinga tunanin ko rayuwar bayan suka yiko kuma samun mutum mai kama sak dawani ya rayu a baya ko masu jin gilmawar tunani a cikin kwakwalwar suna wani abu da ya faru wanda bazasu iya tuna sanda suka aiwatar ba da suaran su.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji bayani daga bakin Sheikh Ibrahim Zakzaky na cewa Mutum zai iya mutuwa ya dawo har ya sake rayuwa a Duniya.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button