Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Tsohon minin fati Muhammad ya bayyana dalilin dayasa Auren su ya mutu.

Tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa kuma miji ga tsohuwar jaruma, Fati Muhammad, Sani Musa Mai Iska ya magantu a kan abun da ya kawo rabuwar aurensu a shekarun baya.

Advertising

Mai Iska ya tuno yadda aurensu ta kasance da Fati wacce suka lula suka bar kasar zuwa Ingila yan watanni bayan bikin nasu sakamakon samun damar shiga wani shiri na wayar da kai kan Kanjamau da ita jarumar ta yi.

Bayan sun yi zama na shekaru uku, sai ya zamana hankalinta ya koma wajen mahaifiyarta da ke gida Najeriya inda shi kuma ya ga ba zai iya barin karatunsa ya koma gida ba saboda ya yi nisa a ciki.

Jarumin ya bayya dalilin dayasa matar tasa ta dawo kasar Nigeriya da zama shi kuma ya zauna a chan kasar Turai, Ya bayyana haka cikin wata hira da jaridau BBC Hausa tai dashi a shirin daga bakin mai ita.

Advertising

Zaku iya kallon cikakkiyar hira a cikin wannan bidiyo da ke kasan wannan rubutun.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button