Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan ta’adda sun kulla kawance da mayakan Boko Haram a jigar Kaduna da Plateau

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ayyukan ta’addancin dake faruwa a yankin Arewacin Nijeriya, ciki har da harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wasu ‘yan bindiga ne da suka kulla kawance da ‘yan kungiyar Boko Haram ne ke aikata wa.

Advertising

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, da takwaransa na yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ne suka bayyana hakan a lokacin da suke zantawa da wakilan yada labarai na gidan gwamnatin tarayya bayan taron majalisar zartarwa na wannan makon.

A cewar Ministocin, duk da cewa hukumomin
tsaro na cigaba da aiki tukuru domin bayyana kungiyar data kai harin, rahotannin farko-farko sun nuna cewa kawancen kungiyoyin ‘yan ta’adda ne ke aikata wa.

Magashi ya ce, a gaskiya ina ganin
shugabannin tsaro suna bakin kokarinsu wajen bankado wadanda ke da hannu a ciki, kuma nan ba da jimawa ba zamu gaya muku wadanda ke kai wadannan hare-hare.

Advertising

Dukkanin hare-haren da aka kai a Jos da Kaduna zamu zo mu bayyana wa jama’a hakikanin abin dake faruwa da kuma kokarin da muke yi na ganin an dakatar da duk wadannan ayyukan gaba daya.

A gaskiya muna kan lamarin muna yin shiri
sosai kuma zamu fitar da shi da wuri.

Shi kuma Mohammed ya kara da cewa, abin dake faruwa a yanzu shi ne akwai wani irin
musabaha mara kyau tsakanin ‘yan bindiga da mayakan Boko Haram.

Rahotanni na farko na abin da ya faru a harin jirgin kasa na Kaduna ya nuna cewa, akwai wani irin hadin gwiwa tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan Boko Haram da aka fatattake daga yankin Arewa maso Gabas.

Zan iya fada muku da kwarin gwiwa cewa, Gwamnatin Tarayya ce ke kan wannan al’amari.

Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button