Advertising
Advertising
Uncategory

Zargin Zamba: Kotun daukaka kara ta bada umarnin sake gurfanar da Abdulsalam Abdulkatim wato A. A Zaura

Zargin Zamba: Kotun daukaka kara ta bada umarnin sake gurfanar da Abdulsalam Abdulkatim wato A. A Zaura

A wani labari da muka samu daga shafin Daily Nigerian Hausa sun ruwauto cewa, Kotun Daukaka Kara a Jihar Kano a ranar Laraba ta yi watsi da hukuncin da wata babbar Kotun Tarayya ta Kano ta yanke, wanda ta wanke Abdulsalam Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani da A. A Zaura.

Advertising

Daily Nigerian Hausa ta tuno cewa, Hukumar
yaki da Cin hanci da Rashawa ta Kasa, EFCC ce ta gurfanar da A. A Zaura, mai neman takarar gwamna a jam’iyar APC a gaban babbar kotun tarayya dake zamanta a Kano bisa tuhume tuhume biyar.

Hukumar ta zargi Zaura da damfarar wani dan kasar Kuwait kudi $1,320,000 bisa zargin cewa yana sana’ar gine-gine a Dubai da Kuwait da sauran kasashen Larabawa.

A ranar 9 ga Yuni 2020 Mai shari’a Lewis Allagoa ya sami wanda ake tuhuma ba shi da
laifi kuma ya sallame shi kan dukkan tuhume-
tuhumen.

Advertising

A bisa rashin gamsuwa da hukuncin da karamar kotun ta yanke, Lauyan dake kare masu kara Musa Isah ya shigar da karar a kotun daukaka kara a wani yunkuri na soke hukuncin da karamar kotun ta yanke.

A wani mataki na bai daya da wasu alkalan kotun daukaka karar guda uku suka yanke kuma mai shari’a Abdullahi M. Bayero ya sanar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.

Bayero ya bayar da umarnin a sake yi wa wanda ake kara shari’a bisa jagorancin wani alkali na daban ba Justice Allagoa ba.

Babban abin da ake ta cece-kuce a cikin daukaka karar shi ne wanda ake tuhuma bai
halarci kotun ba a lokacin da aka yanke hukuncin kuma bisa wasu hukunce-hukuncen da kotun kolin ta yanke, an ce wanda ake tuhuma dole ne ya kasance a gaban kotu a duk tsawon shari’ar da ake yi masa ciki har da yanke hukunci.

A kan haka ne kotun daukaka kara ta samu ikon karba tare da yin watsi da hukuncin baya.

Bayan an tantance batun don goyon bayan wanda ya shigar da kara, a dabi’ance karar ta
yi nasara, An soke karar mai lamba FHCK/CR2018/FRN wadda aka shigar kan
Abdulsalam Sale Abdulkarim wanda aka yanek hukuncin a ranar 9 ga watan Yuli 2020.

Bayero ya kuma bayar da umarnin a mayar da
shari’ar zuwa babbar kotun tarayya a sake fara shari’ar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button