Babu wamda zai sake shiga Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sai yana da Lambar Dan Kasa “NIN”, inji NRC
Babu wamda zai sake shiga Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sai yana da Lambar Dan Kasa "NIN", inji NRC
Fasinjojin dake shirin hawa jirgin kasa suyi maza su tanadi lambar shaidar dan kasa, NIN daga watan Mayu, domin sai da shi za’a shiga jirgin.
Manajan-Daraktan Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen kasa ta Kasa, NRC, Fidet Okhiria, ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Alhamis inda ya bayyana cewa, za’aa bukaci NIN din ne domin inganta bayanan fasinjoji.
A cewar sa, wannan matakin zai kuma inganta kariya da kuma tsaro na masu amfani da layin dogo.
An fara aiwatar da tsarin hada fasinjoji da NIN din su don inganta bayanan fasinjoji, Wannan matakin gwajin fasinjan zai fara a watan Mayu.
Hukumar NRC ta dakatar da jigilar jirgin na
hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon harin da wasu mahara suka kai ranar 28 ga watan Maris, inda suka kashe da jikkata fasinjoji tare da yin garkuwa da wasu.
Okhiria yace, hukumomin tsaro na cigaba da aiki tukuru domin ganin an ceto da kuma sako dukkan fasinjojin da aka sace.
Ya jaddada cewa, fasinjoji 362 da ma’aikatan
jirgin 20 ne ke cikin jirgin a lokacin da aka kai
harin.