Advertising
Advertising
Labarai

Tun da uwar mijina ta leka mu muna kwanciyar Aure da Danta tafara gaba dani.

Wata mata ta koka akan yadda mahaifiyar mijinta ta dena mata magana bayan ta shiga dakin baccinsu ba tare da kwankwasawa ba, ta tarar da ita da mijinta suna tarayya ta auratayya.

Advertising

Kamar yadda ta bayyana, lamarin ya auku ne bayan surikarta ta kawo musu ziyara na ‘dan wani lokaci, jaridar Pulse ta ruwaito.

Tuko.co.ke ta ruwaito yadda matar ta labarta yadda a duk lokacin da mahaifiyar mijinta na nan take kokarin ganin ta janyo rudani tsakaninta da mijinta.

“A duk lokacin da take nan, tana sa ido akan yadda mijina ke kula dani. Sannan tana tuhumar mijina akan wanne dalili zai bani iko da yawa, musamman wajen yanke shawarar yadda abubuwa ke kasancewa a cikin gidan,” a cewarta, kamar yadda shafin labaran suka yanko maganarta.

“Sai dai ba tare da tsammani ba, naji jinjirina yana tsala kuka. Naso zuwa in dubashi, amma mijina ya rikeni, gami da cewa sai mun gama abunda muka fara kuma ai mahaifiyarsa na tare da jinjirin,” a cewarta.

“Daga nan, ta fara antayo min ruwan zagi, tare da tambayar wacce irin uwa ce ni, gami da kirana da karuwa, da dai sauran sunayen banza. Duk iya kokarin da mijina ya yi don natsar da ita bai yi tasiri ba, har sai da ya yi mata ihu, saboda sai da ta kai min mari.

“Daga ranar har zuwa yanzu bata kara min magana ba. Mahaifiyata ta umarceni da in bata hakuri. Ban san mai zai faru ba idan na bata hakuri saboda ban mata laifi ba.”

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button