Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wata mata ta haihu ba tare da tasan tana dauke da juna biyu ba.

Wata matar aure bata taɓa sanin tana ɗauke da juna biyu ba har sai lokacin da ta ga hannun jaririn ta a cikin robar ɓandaki yayin da take ƙoƙarin ƙwarara ruwa bayan ta gama amfani da shi. Shafin LIB ya ruwaito

Advertising

Lalene Malik, mai shekaru 23, ‘yan’uwan ta sun garzaya da ita zuwa asibitin A&E a Northwick Park Hospital, cikin Harrow, birnin Landan, bayan tayi ƙorafin tana fama da matsanancin ciwon ciki a gidan ta dake a Greenford, west London, ranar 26 ga watan Maris.

Ta bayyana cewa tana shan magungunan hana ɗaukar ciki, sannan kuma tayi gwajin juna biyu har sau biyu a watan Fabrairun 2022 inda su ka nuna bata ɗauke da juna biyu.

Saboda haka kawai sai ta ɗauka cewa ciwon cikin na ta ɓacin ciki ne kawai.

Advertising

Ta abin yayi ƙamari an garzaya da ita zuwa asibiti. A lokacin da take jiran a duba ta a asibitin, Lalene ta shiga banɗakin asibitin, inda mahaifiyar ta Sumra, ta jiyo ta tana rafka kuka wanda hakan ya sanya ta sanar da likitocin asibitin.

Lalene wadda ita ce mai jegon ta bayyana yadda lamarin ya faru.

Na rasa abin cewa, an kai ni wani ɗaki na daban saboda ina ta kuka ni da mahaifiyata.

Abin ban tsoro ne sosai a gare mu sannan naji cewa kamar rayuwata na cikin haɗari Mahaifiyata ta fara kuka sannan ta ce min ‘baki san ina ɗauke da jariri ba? Daganan na rasa abin cewa.

Da na san cewa ina ɗauke da juna biyu da naji daɗin lokutan wajen zuwa siyayyar kayayyakin jarirai. A cewar ta Mijin ta yana ƙasar waje a lokacin sannan yayi matuƙar mamaki bayan ya samu labarin haihuwar.

Ɗalibar wacce take karatun digirin ta na biyu a fannin siyasar ƙasa da ƙasa a jami’ar Roehampton, ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta da niyyar haihuwa inda take shan magungunan hana ɗaukar ciki daga watan Oktoba zuwa Janairu wanda likitan ta ya rubuta mata.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button