Duk iyayen da suke haihuwar ‘yaya basa iya kula da su sai Allah ya hukunta su, cewar Nafisa Abdullahi
Duk iyayen da suke haihuwar 'yaya basa iya kula da su sai Allah ya hukunta su, cewar Nafisa Abdullahi
Ficacciyar jarumar Fina-Finan Hausa wanda ta sami daukaka a cikin shirin nan mai dogon zango “Nafisa Abdullahi”, tayi kira ga masu haihuwar ‘yaya ba tare da kula da su ba da su guji yin hakan.
Jaruma Nafisa ta wallafa sakon ne a shafin ta na sada zumum ta Tuwita a ranar Asabat cikin harshen turanci.
Inda take cewa, ku daina haihuwar ‘yayan da kuka san baku da halun kula da su, ta kara da cewa, Allah zai tuhumi Mutanen da suke haifar ‘yaya ba tare da sauke nauyin da ya dora musu ba.
A cewar Nafisa Abdullahi: Kun ga dukkan Mutanen dake haifar ‘yayan da basu ji basu gani ba domin kawai su aika da su Almajiranci, kuma su cigaba da haifar karin ‘yaya Allah sai ya sakawa yaran nan.
Sannan kuma, Nafisa Abdullahi ta bayyana bacin ranta kan yadda wasu Iyayan suke rura ‘yayan su ‘yan shekaru biyu zuwa uku Almajiranta.
Sai dai jaruma Nafisa bata ambaci sunayen wadanda take yiwa wannan gargadi ba, wanda dama ba saban abu bane a kasar Hausa Iyaye suna tura yaran su kanana Almajiranta ba.
Wannan al’amarin na tura kanana yara makarantar Almajiranta ba karamin batawa Mutane rai yake ba, inda wasu na ganin cewe ana amfani da irin wadannan yaran wajan aikata laifuka.