Advertising
Advertising
Labarai

Turkashi: Namijin daya koma mace ya yiwa Mata 2 ciki a gidan gyaran hali na mata.

Wani da aka haifa a matsayin namiji wanda daga bisani ya koma mace ya dirkawa wasu matan gidan yarin da yake ciki juna biyu, kasancewar an killacesu tare.

Advertising

Wasu mata guda biyu a gidan yarin New Jersey sun dauki ciki bayan sun amince da lalata da wani da ya koma mace, shafin Instablog ya ruwaito.

Budirwa ta labarta yadda Dan daudun ya ciki galaba a gareta

Demi Minor ta amince da zama wacce ke da alhakin dirka wa fursinonin ciki, ta wani shafi Justice 4 Demi, wanda take kula da shi daga gidan yarin da take.

Advertising

Shafin labaran ya ruwaito yadda gidan yarin ya kunshi fursunoni 27 wadanda aka haifa a maza, amma daga baya suka koma mata.

An maidasu gidan yarin ne a shekarar 2019 bayan shigar da karar da ACLU tayi, bayan wata mata da aka haifa namiji ta fuskanci cin zarafi daga gidan yarin maza.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button