Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnonin Nageriay sun bada tallafin Naira Miliyan 50 ga wadanda harin Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya shafa

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, NGF, a ranar Juma’a ta bayar da gudunmuwar Naira Miliyan 50 ga gwamnatin jihar Kaduna, domin rabawa wadanda harin bam din da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su.

Advertising

Wata sanarwa da Kakakin kungiyar, Abdulrazak Bello-Barkindo, ya fitar a Abuja a ranar Juma’a ta ce, Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya bayar da wannan gudummawar a lokacin da ya jagoranci tawagar mutane biyu na kungiyar zuwa jihar Kaduna.

Fayemi yace, tawagar ta je jihar ne domin jajanta wa gwamnati da jama’a kan harin jirgin kasa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, yayin da aka kuma yi garkuwa da wasu da yawa.

Shugaban NGF a lokacin da yake jawabi ga Gwamna Nasiru El-Rufai, ya jajantawa jihar
Kaduna da al’ummarta.

Advertising

Ya bayyana harin a matsayin mai tayar da hankali matuka, sabida yawan wadanda suka rasa rayukan su da kuma jikkata.

Fayemi yace, Abin takaici ‘yan ta’addan sun
jajirce wajen ganin sun yi garkuwa da wasu da suka tada zaune tsaye a cikin halin rashin tsaro, wanda ya jefa Kaduna cikin rudani.

Gwamnan na Ekiti ya nuna mamakin cewa, ko
wasu makiya gwamnatin jihar ne ko kuma
gwamnanta ne ke kokarin kawar da jihar daga turbar cigaba.

Fayemi ya yi takaicin cewa, a halin yanzu komai dai koma menene ana tunkarar 2023 yana mai ba da shawarar cewa, ya kamata a kara kaimi wajen tabbatar da tsaron kasar.

Yace, a shekarun baya yankin Arewa maso Yammacin kasar nan ya kasance yankin natsuwa da fahimtar juna.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button