Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yusuf Saseen wanda aka fi sani da Lukman na shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano

Yusuf Saseen wanda aka fi sani da Lukman na shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano

Jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa, Yusuf Saseen wanda ake yiwa lakabi da Lukman a cikin shirin Labarina mai dogon zango, ya tsaya takarar siyasa a jihar Kano.

Advertising

A wani rubutu da abokin Jarumin kuma Darakta a Kannywood, Sulaiman Bello Easy, ya saki a shafinsa na na sada zumunta instagram, ya nuna jarumin zai nemi takara karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

A fastar takara da ta karade shafukan sada zumunta musamman instgaram, Lukman Na Labarina, ya tsaya takarar dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Kano Municipal a zaben 2023 dake tafe.

Darakta Sani Easy yace: Duk da ba na siyasar PDP amma dole na yi wa abokina kara na tallata shi saboda ingancinsa da sanin mutuncin al’umma, bana jin ko a wace jam’iyya ya fito zan ƙasa hidimta masa.

Advertising

Duba da gudummuwar da yake bai wa al’umma ta kowane ɓangare, a gaskiya ya cancanta, muna barar kuri’un ku da kuma fatan Nasara.

Cikekken asalin Yusuf Saseen

Ciakkken sunansa shine, Yusuf Muhammad Abdullahi, amma an fi saninsa da Yusuf Saseen, haifaffen jihar Kano ne wanda ya ta so a cikin jihar, ya yi karatun Firamare da Sakandire a Kano.

Fitaccen Jarumin, wanda ya shahara bisa rawar da yake takawa a shirin ‘Labarina mai dogon Zango’ a matsayin ɗaya daga cikin Samarin Sumayya, ɗan asalin Anguwar gini ne ta cikin garin Kano.

Bayan kammala karatun Digirinsa a Jami’ar Bayero, Lukman ya yi aikin bautar ƙasa NYSC a jihar Nasarawa, daga bisani ya shiga harkar shirya fina finai ta Kannywood.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button