Advertising
Advertising
Labarai

Fahad tsohon mijin jaruma mai kayan Mata ya tona mata asiri kan yaudarar mutane da take

Fahad tsohon mijin jaruma mai kayan Mata ya tona mata asiri kan yaudarar mutane da take

Fahad wanda tsohon mijin Jaruma mai sayar da kayan mata ne ya bayyana wa duniya cewa, sabida dan da suka haifa ne kadai yake tanka mata.

Advertising

Matashin ya bar jaruma duk da yadda ta dinga cika baki akan kayan sana’arta inda yace, kayanta basu da wani tasiri.

Fahad ya shawarci Jaruma da ta dena yaudarar mabiyanta kuma ta kiyaye sanya shi a cikin karairayinta tana tallata hajarta.

Fahad ya cigaba da cewa, abu daya ne kadai yasa yake danne zuciyar sa yake magana da ita wannan dan da suka haifa, amma ta daina yaudarar mabiyan ta.

Advertising

Fahad ya wallafa hotunan wasu sakwanni da ya turawa jaruma na jan kunne akan ta daina masu siyayya a wajan ta.

Inda ya kara da cewa, duk kayan matan ta basa aiki domin shi bai ga alama ba, sannan kuma asirce-asircen ta basu yi aiki akan sa ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button