Advertising
Advertising
Labarai

Shahararran mawakin Koriya ta Kudu yayi aikin Ummara bayan ya Musulinta a shekarar 2020

Shahararran mawakin Koriya ta Kudu yayi aikin Ummara bayan ya Musulinta a shekarar 2020

Shauki ya tashi sosai lokacin da fitaccen
mawakin nan na kasar Koriya ta Kudu, Daud
Kim ya isa Makka domin gudanar da aikin Ummara.

Advertising

A shekarar 2020, Daud, wanda aka fi sani da Jay Kim, ya bayar da sanarwar ba zata a dandalin sa na sada zumunta cewa ya yanke shawarar shiga addinin Musulunci.

Da ga baya ya canza sunansa daga Jay zuwa
Daud.

Bayan annobar korona, sai ya yanke shawarar shiga aikin Ummara, inda ya shiga shafinsa na instagram ya rika saka hotuna da kuma wallafa sakuna daban-daban.

Advertising

Daga nan ne Dauda ya saka jerin hotunansa a
Masallacin Harami a dakin Ka’aba da faifan bidiyo na kewayen masallacin.

A karshe na zo Makka. Nine nafi kowa sa’a domin Allah SWT ya zabe ni ya kawo ni. Masha Allah, ya wallafa a shafinsa.

Yace ya yi addu’a ga daukacin al’ummar musulmi na duniya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button