Advertising
Advertising
Labarai

An gwangwaje matukin adaidaita sahu da miliyan 3 sakamakon zalintar sa da Yan sanda sukai.

Hukumar ‘yan sanda ta baiwa wani direban Dan sahu mai suna Dayyabu Auwalu diyyar Naira miliyan uku.
Hakan ya biyo bayan umarnin wata babbar kotun tarayya da ke Kano, bayan da wasu ‘yan sanda suka far wa Auwalu a yayin da yake gudanar da harkokinsa.

Advertising

Jami’an ‘yan sandan da kotun ta samu da laifin sun hada da Abdullahi Daura da tsohon DPO na ofishin ‘yan sandan Kuntau da ke Kano, CSP Abdullahi.

Da yake sanar da hakan a shafin sa na Facebook, lauyan Auwalu, Barista Abba Hikima ya ce, “muna fatan hakan zai zama izina ga sauran jami’an ‘yan sanda da ke cin zarafin jama’a, da kuma ita kanta hukumar.”

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button