Advertising
Advertising
Labarai

Matukar ba’a biyani diyar matata ba saina halaka mutun 300 cewar wani dan bindiga dake Zamfara.

Wani Gagarumin dan bindiga da ake kira da Nasanda, ya fitar da wani wa’adi ga gwamnatin jihar Zamfara da ta biya shi Naira miliyan 30.

Advertising

Yace za’a biya shi kudin ne a matsayin fansa ga kisan da aka yi wa matarsa da kuma wasu yan uwansa guda biyu.

Dan bindigan ya ce, idan ba’a biya shi wannan kudin ba, to zai kashe mutum 300, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Nasandan yayi ikirarin cewa, ‘yan bijilanti ne suka kashe amaryar sa, kawunta da matar kawunta.

Advertising

A rahoton jaridar, ance ya fitar da sakon ne ta hanyar nadar sakon murya.

“Idan da nayi zari, to da sai in nemi a bani miliyan 50 akan ko wanne mutum da aka kashe mini”

“Kwanaki 14 kawai na bayar a biya min bukatu na ba wai watanni ba, ba kuma zamu kai hari ba sai mun tabbatarda mutane sun fita noma a gonakin su. Idan ba’a bar fulani sun wataya ba, muma sai mun hana kowa sakat.

” Idan gwamnati ta kasa biyan kudin, to zanyi abin da na saba yi, inda zan kashe mutane 300 domin fansa ga rayukan amarya ta, da yan uwanta guda biyu”.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button