Jaruma Hadiza Gabon tayi martani ga masu cewa tana riya a taimakon mutane da take
Jaruma Hadiza Gabon tayi martani ga masu cewa tana riya a taimakon mutane da take
Sanin kowa ne Hadiza Gabon na daya daga cikin
jarumai a masana’antar Kannywood dake da zuciyar taimako wanda ba sau daya ba ba sau biyu ba, jarumar tasha taimakawa bayin Allah da ke cikin damuwa ta hanya biya musu bukatar su ba tare da bata lokaci ba.
cikin irin taimakon da Hadiza Gabon tayi da ya
dauki hankali shine na wani dattijo mai suna
Abba Babuga da ruwa ya cinye gidan sa yana zaune a cikin ruwa ba shi da inda zashi, kuma kudin ginawa Hadiza gahon din ta dauki nauyin gina masa gidan.
Haka zalika akwai wani Datijo da aka taba yada
videon sa yana bayyana soyayyar sa ga Hadiza Gabon din, wanda maimakon hadizan ta nuna bacin rai sai ta fahinci yana bukatar taimako dan haka ta aika masa da naira 200k.
Gami da bayyana masa shi ai uba yake a gare ta indan auren ra yazo zata sanar masa, wanda wannan na mutukar burge masoyanta da sauran al’umma.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sauran bayanan jarumar.