Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mawaki Rarara ya gwangwaje Hassana Muhd da kyakkyawar Mota/Tarbiya tun daga gida take farawa, cewar Rahma Sadau

Mawaki Rarara ya gwangwaje Hassana Muhd da kyakkyawar Mota/Tarbiya tun daga gida take farawa, cewar Rahma Sadau

Kamar yadda kuka sani a watan da ya gabatane a cikin bajakolin auratayya da masana’antar kannywood tayi ne akayi auren jaruma hassana muhammad da furodusa abubakar mai shadda inda bayan auren nasu kuma akaji cewar sun tafi kasar dubai yawan shakatawa amma tare da wasu daga cikin jaruman kannywood.

Advertising

Inda a cikin wayanda suka halirchi wannan shakatawar rarara yana daya daga cikinsu ,saide kuma anji cewar sun dawo gida nijeriya inda bayan dawowarsu muka sami wallafawar da hassana din tayi na cewar rarara ya gwangwajeta da sabuwar mota tare da yi masa godiya kamar haka.

To Alllah ya sanya da alkairi a wani bangaren kuma jiyane aka karade kafar sadarwa da cece kuce kan maganar da rahma tayi a shafin na twitter inda tace ‘CHARITY BEGINS AT HOME’ wadda ma’anar haka da hausa na nufin tarbiya tun a gida take somawa.

Advertising

Saide koda da mabiyan jarumar suka ga wannan wallafa sun fara mayar mata da maganganu kan irin yadda take shigar da bata dace ba da kuma rukumai rukumai maza, wato itama haka tarbiya da ta samu daga gidansu kenan kasancewar ita musulma ce kuma bahausa inda addini da al’adar bahaushe bata aminta da irin tata tarbiyar ba.

https://youtu.be/cABnJ7lEspY

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button