Labarai

Shugaba Buhari ya bayyana cewa Gwamnatin sa tafi samar da tsaro a kan ta Goodluck Jonathan

Shugaba Buhari ya bayyana cewa Gwamnatin sa tafi samar da tsaro a kan ta Goodluck Jonathan

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake
bayyana cewa, gwamnatin sa tafi samar da tsaro a kan lokacin mulkin Goodluck
Jonathan.

Buhari ya bayyana hakan ne a taron Kwamitin Koli na Kasa na APC a jiya Laraba a Abuja.

Premium Times ta rawaito cewa, Buhari yace
yanzu an fi samun matsalar tsaro a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda yace Arewa maso Gabas ta samu zaman lafiya yanzu.

Sai dai kuma Shugaban ya tabbatar da cewa,
zai yi amfani da irin salon da ya yi na yakar Boko Haram a Arewa maso Gabas wajen samar da zaman lafiya a Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Gabas.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, Buhari
ya yi ikirarin ne yayin da yan fashin daji, ISWAP da IPOB ke cin karensu ba babbaka a kasar nan, inda a kulli yaumin sai an samu rahoton kashe-kashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button